Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya sha alwashin daukar mataki da kan sa kan kisan gillar da aka yi wa Hanifa, yarinyar da aka yi garkuwa da ita kuma daga bisani aka kashe a Kano.
Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar da Hanifa ke zuwa, ya tabbatar da kashe yarinyar bayan ya yi garkuwa da ita a watan Disamba Shekarar bara ta 2021.
A wata takardar da hadiminsa na fannin yada labarai, Sule Yau Sule ya fitar a shafin sa na Facebook, Shekarau ya jajanta wa iyayen yarinyar tare da shan alwashin sai ya bi mata kadin ta.
“Wannan kisan rashin imanin ba za mu bar shi ya tafi haka ba”, inda ya sha alwashin bibiyar lamarin har sai ya ga karshen sa. Shekarau ya yi fatan Allah ya bai wa iyayen Hanifa juriya da hakurin wannan rashin.
