2023: Na Yi Wa Najeriya Tsufa A Zama Shugaban Kasa – El Rufa’i

Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana cewa Najeriya tana bukatar Shugaba ne mai jini a jika ba tsoho ba, inda ya kara da cewar aikin shugabancin kasa ga mai shekara 62 wahala ce kawai.

El Rufa’i ya fadi hakan yayin da yake amsa tambayar cewa ko yana shirin zama Shugaban Kasa a 2023 a hira da sashin BBC Pidgin ya yi dashi a karshen mako.

Gwamnan ya ce aikinsa na gwamnan jiha guda daya rak na masa nauyi barin ma a yi maganar shugabancin Najeriya, A cewarsa, nauyin zamansa gwamna kawai ya sanya kansa gaba daya ya yi furfura cikin shekara shida ina ga ace yana rike da akalar shugabancin ?asa gaba daya.

“Ka dubi furfurar kaina. Idan ka dubi hotuna na sanda aka rantsar da ni, sumar kaina baka kirin take lokacin; amma duba yadda yau ta zama yanzu. Aiki ne gagarumi kuma a hakan ma wai gwamna ne kawai — jiha daya cikin jihohi 36.

“Gagarumin aiki ne, kwarai; sannan mawuyaci, eh, amma wai a hakan ma ba za ka kwatanta shi da Najeriya ba. Shugabancin Najeriya ba aikin kawai ba ne, ya fi gaban mai shekara 62.

An tambaye shi ko yana da sha’awar zama mataimakin shugaban kasa, sai ya kada baki da cewa: “Ban taba tunanin wannan ba ko kadan. Na fada a baya can cewa a irin tsarin siyasarmu bayan Shugaba Buhari ya kammala shekara takwas na wa’adinsa, ya kamata Shugabancin ya koma Kudanci.”

Related posts

Leave a Comment