Siyasa: Sarkin Yakin Atiku Ya Yi Mishi Tawaye

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben 2019, Prince Kassim Afegbua, ya shawarci ‘yan jam’iyyar PDP da su mika tikitin takarar shugabancin kasa na jam’iyyar zuwa kudu a maimakon bai wa Atiku saboda yawan shekarun sa.

A wata takarda da tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Edo ya fitar, ya ce kamata ya yi Atiku ya hakura da neman kujerar shugaban kasa kuma ya bai wa dan takarar kudu goyon baya domin tabbatar daidaito da adalci a tarayyar Najeriya.

Ya ce zai kasance mai suka tare da rashin goyon baya ga kowanne dan takarar arewa da ya nuna sha’awar zama shugaban kasa a zaben 2023 a cikin jam’iyyar PDP. Ya shawarci kwamitin ayyukan kasa na jam’iyyar karkashin shugabancin Dr Iyorchia Ayu a su duba matashin dan takara.

“Ganin rashin kwazon da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna saboda shekarun sa, rashin dacewa da kuma rashin isa da gogewar siyasa wurin tsamo kaasar nan daga dukkan kalubale, akwai rashin dacewa a ce Alhaji Atiku Abubakar zai cigaba da nuna bukatarsa ta haye wa kujerar shugabancin kasar nan duk da yawan shekarun sa.

“Ba zai yuwu ya cigaba da zama dan takarar jam’iyyar nan ba a kowacce shekara sai ka ce shi aka kafa wa jam’iyyar.

“Babu dabara ko kadan a ce tsohon ya na kokarin sake takara a wannan lokacin da halin da kasar nan ta ke ciki na bukatar matashin dan takara da kuma dan kudu”. “Bayan zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya bar mu a Najeriya inda ya tafi Dubai neman mafaka, hakan yasa muka dinga fuskantar barazana da kalubale tare da hantara daga masu iko a jam’iyya mai mulki.

“Wannan tamkar Janar ne ya bar dakarun sa a filin daga. A maimakon ya dage su samu kwarin guiwa daga wurin shi, rashin sa kuwa ya sa an fuskanci kalubale mai yawa. Ya na Dubai, ya bar mu fayau.”

Related posts

Leave a Comment