Isra’ila Ta Zargi Falasdinu Da Lalata Kabarin Annabi Yusuf


Rahotannin dake shigo mana daga ?asar Isra’ila na bayyana cewar Mahukuntan ?asar sun ce Falasdinawa sun lalata wani wuri mai tsarki na Yahudawa a Nablus, a yayin da rikici ke ?ara ?amari tsakanin Falasdinawa da sojojin Isra’ila a yankin gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

Wani shafin Twitter na gwamnatin Isra’ila ya wallafa wani bidiyo da ya ce ke nuna yadda Falasdinawa ke kai hari a wurin da Yahudawa ke ganin ya ?unshi ?abarin Annabi Yusuf.

Zuwa yanzu babu wani martani daga ?angarorin Falasdinawa.

Yahudawa na girmama wurin da ?abarin yake, amma yana cikin yankin Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

An sha yin arangama a wurin, har ta kai aka ?ona kafin aka sake gyarawa.

Ministan tsaron Isra’ila Benny Gantz ya bayyana al’amarin a matsayin “babban laifin sa?a ?ancin ibadah.”

Yankin Yamma da Kogin Jordan na fuskantar barazanar tsaro tun bayan farmakin da sojojin Isra’ila suka ?addamar bayan harin da aka kai a Tel Aviv da kuma cikin yankin Isra’ila.

Related posts

Leave a Comment