Yobe: Iyalan Wadanda Jirgin Yaki Ya Hallaka Suna Neman Diyya

Rahotanni daga Jihar Yobe na bayyana cewar Iyalan wadanda mummunan lamarin da ya faru a jihar Yobe da su sakamakon luguden wutan da jirgin ya?in rundunar sojin sama ya so yi kan ‘yan ta’addan Boko Haram, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta biya su diyya.

Sun alakanta bukatarsu da dalilin cewa, gwamnati a kowanne mataki a Najeriya ba ta cika biyan diyya ba ga jama’a da aka yi wa barna, sai dai kawai a barsu cikin damuwa.

Daga ciki mutum takwas da suka rasu, tsoffafi uku da wata mata wadanda suka bar kananan yara. Akwai yara kanana hudu da suka rasa rayukansu da kuma wasu gidaje da suka kone.

Yayin da wasu wadanda lamarin ya ritsa da su ke hanyarsu ta zuwa gona, wasu ya ritsa da su ne suna kan hanyar zuwa kasuwar mako ta Geidam.

Wasu mazauna yankin sun yadda cewa wannan harbi da aka yi wa farar hulan bisa kuskure ne. Sun ce duk da haka lamarin Allah ya tsaro, suna bukatar a biya su diyya bayan tallafin maganin da ake basu.

Rundunar sojin saman Najeriya ta amince da cewa jirgin ta ne yayi wa jama’a ruwan wuta amma bisa kuskure bisa ga haka suna neman afuwa.

An ruwaito cewa, kamar wasu lamurra irinsu da suka faru, rundunar sojin saman ba su taba batun diyya ba duk da sun ce an kafa kwamitin bincike a kan lamarin.

Related posts

Leave a Comment