Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce Rasha ta kai hari kan asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya 60a yayin mamayar da ta ke yi a Ukraine.
Hukumar ta tabbatar da cewa an kashe mutum 15 a hare haren, a yayin da aka raunata akalla 37.
Jami’an lafiya a iyakoki sun ce mutane na fama da karancin abinci da ruwan sha kuma suna cikin wahala, yayin da wasu kuma ke tafiyar kwana da kwanaki ba tare da maganin da suke bukata ba.
Sakamakon wani binciken gaggawa da hukumar lafiya ta duniya ta yi ya nuna cewa a cikin ‘yan gudun hijra rabin miliyan, kusan dubu dari biyu da hamsin a cikinsu da suka isa Poland na fama da matsananciyar damuwa wadda ke bukatar kulawar gaggawa.
Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce fiye da mutum miliyan uku da rabi suka bar Ukraine ya zuwa yanzu.
