Tausayin ‘Yan Najeriya Ya Sa Na Fito Takara – Atiku

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abukabar ya ce ?an Najeriya ne suka bu?aci ya tsaya takarar shugaban ?asa a shekarar 2023.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata kwana guda kafin ya ayyana takararsa a hukumance.

Atiku ya ?ara da cewar ya zai tsaya takara ne a 2023 domin kawo wa ?an Najeriya sau?i kan matsalolin da suke fuskanta musamman abin da ya kira “rashin ha?in kan ?asa.”

Da aka tambaye shi ko yaya zai yi da sauran abokanan takararsa na PDP, Atiku ya ce ba su da wata matsala a jam’iyyar domin kuwa idan suka zauna za su fitar da ?an takara cikin ruwan sanyi.

“Idon muka shiga daki muka zauna zamu fita mu kuma fitar da ?an takara babu wata matsala.”

Da yake Magana kan matsalar tsaro Atiku ya ce rashin zaman lafiya da kasar ke fuskanta abun takaici ne.

‘Babu shakka akwai matsalolin rashin zaman lafiya kuma wa?annan abubuwan sun faru ne don rashin shugabanci’.

Related posts

Leave a Comment