Da Dumi-Dumi: Babban Banki Ya Umarci Bankuna Su Karbi Tsoffin Kudi

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya umurci dukkan bankunan Najeriya su fara karban tsaffin kudaden N1000 da N500 daga hannun jama’a yanzu.

Gwamnan ya bayyana cewa ya canza shawarar cewa kowa ya kai CBN kadai, bisa wani sharadi, sharadin shine mutum N500,000 kadai zai iya kaiwa bankunan.

Duk kudin da ya wuce N500,000 mutum ya kai bankin CBN,Diraktan Sadarwa na bankin, Osita Nwanisobi, ya tabbatar da labarin inda ya bayyana cewa: “Kawai na masu N500,000 da abinda yayi kasa ne.”

Related posts

Leave a Comment