Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar kwamitin yana binciken zargin take hakkin dan Adam da rusasshiyar rundunar yaki da fashi da makami (SARS) da wasu sassan ‘yan sandan Najeriya ke yi.
Kwamitin bincike ya aike wa Abba Kyari sammaci, an sanar masa ranar da zai gurfana. Masu shigar da kara, Ambrose Mairungu, da Blessing Dung, a cikin wata kara mai lamba 2020/IIP-SARS/ABJ/205 sun yi zargin cewa Yakubu Danjuma, Ibrahim Daniel da Choji, an kama su ba bisa ka’ida ba tare da tsare su, azabtarwa da kuma cin mutuncin duk kuma Kyari ne yayi hakan.
A ranar 11 ga watan Maris kwamitin binciken ya umurci shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA mai ritaya, Brig.-Gen. Buba Marwa zai fito da Kyari a ranar 22 ga Maris, don kare kansa.
Sai dai a martanin da aka bayar ga wannan umarni, Abdullahi Haruna, SAN, lauyan Kyari ya rubuta wasikar gudanarwa ga shugaban kwamitin. Yana neman a gabatar da duk koke-koke da aka ambaci sunan Kyari don ba shi damar yin nazari da kuma amsa su yadda ya kamata.
Don haka ya roki kwamitin da ya ba shi watanni biyu domin yin nazari akan tuhume tuhumen da ake yi wa Kyarin.
A ?angaren su Garba Tetengi, SAN, wanda ya wakilci shugaban kwamitin Mai shari’a Suleiman Galadima mai ritaya, ya ce kwamitin ba shi da lokaci amma zai iya ba shi mako guda.
