Rana Ba Ta Karya: Yau APC Ke Gudanar Da Taron Gangamin Jam’iyya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yau ne jam’iyya mai Mulki ta APC ta shirya gudanar da gangamin taron jam’iyyar na ?asa domin za?en sabbin shugabannin da za su ja ragamar jam’iyyar.

Shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan jama’a na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya ce APC ta shirya jerin sunayen hadin kan taron gangamin jam’iyyar da zai gudana yau Asabar.

Sule ya tabbatar da cewa tuni wasu shiyyoyin siyasar kasar nan suka amince da jerin sunayen da za a hada su domin fuskantar babban taron jam’iyyar.

Shugaban kwamitin yada labaran ya kuma tabbatar da cewa tsarin yarjejeniyar ya kasance zabin farko na zaben sabbin shugabannin jam’iyyar.

“Daga abin da muke da shi a yankuna daban-daban, jerin hadin kai zai kasance a shirye wanda za’a mika shi yau.

Related posts

Leave a Comment