Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai kan ?auyuka shida a ?aramar Hukumar Giwa ta Jihar sun yi sanadiyyar kashe adadin jama’a masu yawa.
Ma’aikatar tsaro ta jihar ta tabbatar da kai harin a ranakun Alhamis da Juma’a amma ba ta bayyana adadin wa?anda aka kashe ba, tana mai cewa suna jiran cikakken rahoto kan lamarin.
Wasu rahotanni na cewa an kashe mutum kusan 50 a hare-haren.
Garuruwan da lamarin ya shafa sun ha?a da Dillalai, da Barebari, da Dokan Alhaji Ya’u, da Durumi, da Kaya da kuma Fatika.
