Wani rahoto dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar Fasto Isaac Moses na cocin Amazing Revelation Divine Ministry, Suleja, ya gargadi mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, kada ya yaudari Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a za?en dake tafe.
Faston ya bayyana cewa idan Osinbajo ya yaudari Tinubu, hakan na iya zama karshen siyasarsa. Ya shawarci Osinbajo cewa yaudara zunubi ne kuma a matsayinsa na Fasto ya san da haka.
“Idan kayi, zaka ji kunya wajen mutane, kuma mutuncinka ya zube.” “Kamar yadda aka min wahayi, akwai karshe mara kyau idan Osinbajo ya nemi takara. Abun ba zai yi kyau ba.”
“Osinbajo namu ne. Kiristoci na son sa kuma suna ganin girmansa. Amma abubuwan dake faruwa kwanan nan da ban damuwa.” Kada ka yaudari Tinubu, idan ba haka karshenka ba zai yi kyau ba.
Faston ya cigaba da cewa shin wani dalili ya hanashi fitowa fili ya fadi cewa bai da niyyar takara don kashe wutan jita-jitan dake yawo?
“Misali, ya ki fitowa ya karyata labaran niyyar takara. Wannan ba halin Kirista bane. Ya kamata ace yayi bayani.” “Duk da Tinubu Musulmi ne, shine babban wanda ya tsayawa Osinbajo tsawon shekaru”.
