Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Bun?asa Tattalin Arzikin ?asashen Afirka ta Yamma ECOWAS, sun garga?i Najeriya kan batun haddasa rikici a za?en ?asar na 2023 da ke tafe.
Sun bayyana hakane a wani taron tattaunawa da kungiyar shiga tsakani na jam’iyyu da masu ruwa da tsaki da suka fito daga yankin arewa ta tsakiya da arewa maso gabas kan kaucewa tada fitina a Jos, babban birnin jihar Filato a ranar Talata.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce muddin ba a ?auki mataki ba, za a iya samun rashin zaman lafiya a fa?in yankin.
Ita ma ECOWAS ta ce idan rikici ya ?arke a Najeriya, babu wata ?asa a yankin sahara da za ta iya bai wa ‘yan gudun hijirar ?asar mafaka saboda yawansu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sama da mutane 30 ne aka ruwaito mutuwarsu yayin da da yawa suka jikkata a rikice-rikice gabanin za?en 2023 a sassan daban-daban na Najeriya.
An kuma kai wa ofisoshin hukumar za?e mai zaman kanta hare-hare a wasu sassa na Najeriya musamman ma kudu maso gabas, inda ake zargin kungiyar ‘yan awaren Biafra da kai hare-haren wanda ya yi sanadiyyar rasuwar jami’an INEC da kuma jami’an tsaro da dama.
