Jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara sun kai ?arar ministan shari’a Abubakar Malami, da gwamnan Babban Bankin Godwin Emefiele, saboda zargin ?in bin umarnin kotun ?olin kan wa’adin amfanin tsofaffin takardun ku?i.
A wata sabuwar ?ara da suka shigar gaban kotun, jihohin uku sun garga?i ministan shari’a na ?asar ga gwamnan CBN ?in kan ?in bin umarnin hukuncin da kotun ta yanke ranar 3 ga watan Fabrairu.
Jihohin sun ce aiwatar da tsarin ya jefa al’umomin jihohinsu cikin mawuyacin hali.
A ranar 8 ga wata ne kotun ?olin ?asar da takatar da CBN daga wa’adin da ya sanya na daina amfani da tsofaffin takardun ku?in ?asar, bayan da jihohin uku suka shigar da ?ara suna ?alubalantar wa’adin.
To sai dai ministan shari’a wanda shi ne ke wakiltar gwamnatin tarayya a shari’ar ya ce kotun ?olin ba ta da hurumin shiga cikin lamarin.
Sannan kuma Malami ya ce masu shigar da ?arar ba su sanya CBN cikin ?arar ba.
Daga baya ne kuma jihohi bakwai suka shiga cikin jerin jihohin da ke goyon bayan jihohin uku, a yayin da johohi biyu suka mara wa gwamnatin taraya baya.
