Sarkin Musulmi Ya Ayyana Yau Laraba A Matsayin Daya Ga Watan Sha’aban

Fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar lll ta sanar da ranar Laraba a matsayin 1 ga watan Sha’aban.

A wani sa?o da sarkin malaman Sokoto, kuma sakataren kwamitin ganin watan Malam Yahaya Muhammad Boyi ya aike wa da BBC ya ce mai alfarmar sarkin musulmin ya tsayar da ranar Laraba a matsayin 1 ga watan Sha’aban.

Tun da farko dai kwamitin ganin wata na mai alfarma sarkin Musulmin ya wallafa a shafinsa Tuwita cewa kasancewar ba su samu labarin ganin jinjirin watan ranar Litinin ba za a cike Talata a 30 ga wata.

Mai Alfarma sarkin musulmin ya sanar da ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu a matsayin ranar 1 ga watan Sha’aban.

Ganin watan na Sha’aban, abu ne mai matu?ar muhimmanci ga al’ummar Musulmi, saboda shi ne watan ?arshe kafin na Ramadan, wata mai tsarki da ake azumi tsawon kwana 29 ko 30.

Related posts

Leave a Comment