Duk Wanda Na Kora Daga Aiki Ya Tafi Har Abada – El Rufa’i

Rahoton da muke samu daga fadar mai girma Shugaban kada dake birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna, ya yiwa shugaban ?asa Buhari cikakken bayani kan kudirin gwamnatinsa na yin garambawul da kuma matakan da ya ?auka na aiwatarwa a fadin Jihar Kaduna.

Gwamnan yace gwamnatinsa zata bu?aci bayani kan matakin da ?ungiyar kwadugo ta ?auka, inda zata kafa hukumar da zata binciki yajin aikin NLC da zanga-zngar da ta gudanar a watan Mayu 2021.

El-Rufa’i ya tabbatarwa shugaba Buhari cewa, gwamnatinsa ba zata sake bari a maimaita halin da mutanen jihar suka shiga na ?unci, matsin tattalin arzi?i da hana su ‘yancin su, wanda NLC ta jawo musu ba.

A wani jawabi da mai baiwa gwamna shawara ta musamman kan ya?a labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar, El-Rufa’i yace yanzu haka gwamnatinsa ta fara aikin ?aukar ma’aikata 10,000. Yace wannan duk yana cikin tsarin gwamnatinsa na aiwatar da garambawul, inda zata cigaba da ?aukar kwararrun malamai, likitoci, masu jinya da kuma ma’aikatan da suka cancanta domin gudanar da aiki mai kyau a jihar.

Related posts

Leave a Comment