Uwar gidan shugaban ?asa Aisha Buhari ta ce ta bayar da umarnin a goge wani labari da ba na gaskiya ba da ya bayyana a shafinta na sada-zumunta.
Da safiyar ranar Talata ne dai aka wallafa wata sanarwa ta boge da aka al?anta da CBN a shafukan Facebook da Instagram na Aisha Buhari, inda aka bayyana ?ara wa’adin amfani da tsofaffin takardun ku?in ?asar har zuwa 1 ga watan Maris mai zuwa.
To sai dai a wata sanarwa da Babban Bankin ?asar ya fitar, ya garga?i masu ya?a wannan labari.
Cikin wani sa?o da Aisha Buhari ta wallafa a shafinta na Instagram, ta ce wannan ba shi ne karon farko ba da ake yi wa shafin nata kutse.
”Wannan mutumin mai kutse ne, kuma mai mummunar zuciya da ke da aniyar ?ata min suna ta hanyar amfanin da shafukana na sada zumunta,”
“Amma ina mai tabbatar muku da cewa wannan shi ne karo na ?arshe da zan musanta wani labarin ?arya da aka wallafa a shafina da kaina”, in ji Aisha Buhari.
“Aikin jami’an tsaro ne su gano wanda yake min kutse a shafukana, domin ?aukar matakin da ya dace”, in ji ta.
