Daga ALIYU SULEIMAN
Ba wai girma ake bu?ata ga wu?ar da za a fe?e giwa ba, a’a, mai kaifi ake nema komai ?an?antar ta.
Yayin da ake gwabza ya?in neman za?en gwamnoni a fa?in jihohin Najeriya, za?en da zai kasance cikin sahun gaba wanda za a yi kallon kwatagwangwamar kokawa a Arewa, shi ne za?en gwamnan Jihar Gombe, wanda a cikin ‘yan takara har da Khamisu Mailantarki, wanda jam’iyyar NNPP ta tsayar takarar gwamna a Gombe.
Kada mai karatu ya yi shakku, tababa ko tantama cewa Mailantarki zai iya kayar da Gwamna Inuwa Yahaya a za?en 2023. Wanda bai san Mailantarki ba, shi ne zai tsaya ya na wasiwasin wannan nazari.
Amma babu shakka, a duk inda Inuwa Yahaya zai kwana ya tashi, to ko an ce ba ya tunanin Mailantarki, wannan yaudarar kai ce kawai. Saboda ba shi da ke gwamna ba, a duk Najeriya masu biye da tarihin siyasa sun san tarihin da Mailantarki ya ta?a kafawa a 2011. Yaro na goye ne ka?ai bai san Mailantarki ba.
A za?en 2011, Mailantarki ya fito takarar ?an Majalisar Wakilai ta ?asa a Majalisar Tarayya a ?ar?ashin CPC, jam’iyya maras galihu a lokacin. Me ya faru, talakawa da masu halin ?ananan Hukumomin Gombe/Kwami/Funakaye sun zuba masa ?uri’un da babu wani ?an Majalisa da ya samu kusan yawan ta shi a 2011, kakaf ?in su har su 360 a Najeriya.
Yayin da Mailantarki ya samu ?uri’u 122,987, abokin takarar sa na PDP kuwa ?uri’a 44,206 ya samu. Shi kuma na ANPP ya tashi da ?uri’un da ba su wuce a jefa cikin aljihun riga malum-malum ba, wato guda 8,760 kacal.
Fitar Mailantarki daga APC a cikin watan Mayu, 2022 ke da wuya, sai NNPP ta ba shi takarar gwamna.
Alamomin Mailantarki zai firgita manyan namun dajin siyasar Gombe na cikin gwamnati ta fara ne tun daga lokacin da NNPP ta ba shi takara babu hamayya. Wakilai 342 daga ?ananan Hukumomi 11 duk su ka amince da shi, babu hamayya.
Sannan kuma shi da kan sa bayan ya lashe za?en fidda-gwanin da wakilai 342 ?in zu ka za?e shi, ya ce, “a tarihin Jihar Gombe ba a ta?a yin za?en fidda-gwanin da ya kai na sa zama sahihi ba. Wannan ma alama ce mai nuni da cewa Mailantarki ya samu tagomashi a fa?in jihar kenan.
‘Ba Na Tsoron Gwabza Karo Da Gwamnatin Da Ke Kan Mulki’ – Mailantarki:
A cikin wata tattaunawa da aka yi da shi bayan ya yi nasarar zama ?an takarar NNPP, Khamisu Mailantarki ya ce ba ya tsoron fitowa takara da Gwamna mai mulki, ko kuma gwamnatin da ke kan mulki.
Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne, domin a baya Mailantarki ya nuna cewa shi mutum ne mai jama’a. Su kuma jama’a su ne kasuwa, ba yawan rumfuna ba.
“A baya abu ne mai wahala a fito yin kokawar gaba-da-gaba da gwamna mai mulki a Jihar Gombe. Amma yanzu abu ne mai sau?i, kuma idan mu ka yi gaba-da-gaba, mu ka ha?a ?wanji a ranar za?e, to kayar da gwamna abu ne mai sau?i a wuri na.” Inji Mailantarki, bayan an tsayar da shi takarar gwamna a ?ar?ashin NNPP.
Daga cikin la?anin da Mailantarki ke ta?ama da su, akwai jama’a, wa?anda su ne ya ce su ka ro?e shi ya fito takarar gwamna, domin su sake yi masa irin ruwa da ?an?arar yawan ?uri’un da su ka ta?a yi masa a 2011. Wannan karon ma gaba ?ayan jihar ce, ba wai a ?ananan hukumomi 3 kamar na za?en 2011 ba.
Wani la?anin da Mailantarki ya ce ya ke ta?ama da shi, shi ne i?irarin sa cewa gwamnatin APC ba ta tsinana wa Gwambawa abin a zo a gani har a yaba ba.
Ko ma dai me ke nan, ganin yadda guguwar Mailantarki ke kwashe manya da ?ananan ‘yan APC da PDP, su na watsi da laima da tsintsiya su na rungumar kwandon kayan marmari, hakan alama ce mai nuna cewa za a kwashi ‘yan kallo a ranar kokawar za?en 2023.
Tabbas Gwamna Inuwa Yahaya na da aiki a gaban sa. Kuma duk irin inuwar da Inuwa ya shiga da rana, to zai kasance cikin tunanin hasken Mailantarki. Duk cikin duhun da Inuwa Yahaya ya shiga da dare, sai ya yi tunanin hasken Mailantarki. Kai, ko cikin hasken lantarki ko hasken taurari da farin wata Inuwa Yahaya na APC ya shiga, zai ya ri?a tuna hasken Mailantarki.
Farin jinin Mailantarki zai iya sakar wa sauran ‘yan takara sukuntumau, ta yadda ko haske fitilar cocila su ka gani, su ce hasken lantarkin Mailantarki ne
Wata?ila ma ko a mafarki, ba zai rasa yin mafarkin hasken lantarkin Mailantarki ba.
