Buhari Zai Sayar Da Kadarorin Gwamnati Domin Cike Gibin Kasafin Kudin 2023

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sakamakon girman gi?in da ake da shi a kasafin ku?in shekarar 2023, gwamnatin tarayya ta tsara sayar da wasu daga cikin kamfanonin lantarki don cike gi?in.

Gwamnatin ta ?auki matakin ne yayin da ya rage ?asa da wata shida ta sauka daga mulki.

Za a sayar da kadarorin cikin wata ukun farko na 2023, amma za a bu?e shirin sayar da su a wannan watan na Disamba zuwa ?arshen Maris.

A watan Oktoba da ya gabata Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin na 2023 da ya kai naira tiriliyan 20 (dala miliyan 45) – kasafi na ?arshe kenan da gwamnatinsa za ta yi.

Najeriya kan aiwatar da kasafin ne da ku?in da take samu daga ku?a?en man fetur, wanda farashinsa ya gamu da cikas tun daga shekarar 2020, da kuma satar man da tsageru ke yi a yankin Neja-Delta da ke kudancin ?asar.
Majalisa Ta ?i Amincewa Da Kasafin Ku?in Shekarar 2023

Idan ba a manta ba Majalisar Dattawa ta ?i amince wa da kasafin kudin ?asar na shekarar 2023 a ya yin zaman majalisar na ranar Alhamis.

Shugaban Majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ce rashin amincewa da kasafin ku?in ya biyo bayan kurakurane da kasafin kudin ke kunshe shi, daga ?angaren gwamanti.

“Sakamakon wasu ?alubale, ba za mu iya karbar rahotan kwamitin kula da kasafin kudin ?asar ba saboda, ya zo majalisa da matsaloli.

Ahamd Lawan ya ce sai a jiya majalisar dattawan sun kuma kar?ar ?arin wasu bu?atu daga shugaban Najeriya, na kari a kasafin kudin na wasu ayyukan na musamman na naira tirilliyan 23.7.

Ya ce ranar Larabar 28 ga Disambar da muke ciki, yanzu suka tsayar domin amincewa da kasafin.

Related posts

Leave a Comment