Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mazauna yankin da suka rasa rayukansu yayin musayar wuta tsakanin sojin Najeriya da ‘yan bindiga a karamar hukumar Maru ta jihar.
Gwamnan ya bayyana alhininsa game da aukuwar lamarin a wata takarda da mai bashi shawara ta musamman a lamurran da suka shafi sadarwa, Zailani Bappa, ya fitar a ranar Talata.
Bappa ya ce gwamnan yayi takaicin jin labarin mara dadi yayin da sojin saman Najeriya suka yi fito na fito don sheke kungiyar ‘yan bindiga, amma cikin rashin sa a hakan ya ritsa da wasu mazauna yankin. “Wannan lamarin mara dadi yazo ne a lokaci daya, yayin da sojin saman Najeriya suka fito gaba gadi don kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga, musamman ta hanyar yi musu luguden wuta.
“Zan so a madadin kaina da iyalina, da gwamnatin jiha da dukkan al’ummar jihar Zamfara in mika sakon jaje ga wadanda suka samu raunuka da mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan barnar.”
