Obasanjo Ya Jagoranci Dattawan Yarbawa Wajen Tsayawa Igboho

Dattawan Yarbawa bisa Jagorancin tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo sun tafi kasar Jamhuriyyar Benin inda suke nemawa Sunday Igboho da aka kama sassaucin hukunci.

Obasanjo ya je kasar Benin inda wata majiya tace ya gana da shugaban kasar, Patrice Talon amma dai ba’a san ko sun tattauna maganar Sunday Igboho ba.

Amma dai majiyoyi da yawa na amannar cewa maganar Sunday Igboho ce ta kaishi kasar.

Hakanan a wani Labari me kama da wannan, Abokin fafutukar Sunday Igboho, Farfesa Banji Akintoye ya tsere zuwa kasar Benin Republic bayan da aka yi tsammanin cewa gwamnati na nemansa Ruwa a Jallo.

Related posts

Leave a Comment