Zan Tsaya Takara A Shekarar 2023 – Farfesa Jega

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon shugaban hukumar za?e mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar PRP ne domin ya bada gudummuwarsa a siyasance.

Jega ya kara da cewa zai tsaya takara a za?en 2023 dake tafe amma ya zuwa yanzun bai yanke shawara a kan mukamin da zai tsaya takara ba.

Farfesa Jega ya fa?i haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da sashen Hausa na BBC a karshen makon da ya gabata.

Tsohon shugaban hukumar zaben INEC yace jam’iyyar APC da ta adawa PDP ba su da kwarewar cigaba da jagorancin ?asar nan a yanzu. “Manyan jam’iyyun kasar nan biyu APC da PDP ba su cancanci ci gaba da jagorancin kasar ba, basu da kwarewar da ake bukata.” “Ina kira ga yan Najeriya (kasar da tafi yawan jama’a a Nahiyar Afirka) da kar su sake za?en su a babban zaben 2023 dake tafe”.

Related posts

Leave a Comment