‘Yan Boko Akida Ne Matsalar Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar lll ya bayyana cewa, ‘yan boko akida su ne matsalar Najeriya a halin da ake ciki yanzu, kuma muddin ba a yi gyara ba abubuwa za su cigaba da tafiya ne ba yadda ake so ba.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a jihar Gombe yayin wani taron da ya gudana na addinai a jihar ta Gombe Ya kuma kalubalanci shugabanni da cewa su koma ga littafan addininsu domin samun mafita da cimma nasarar da ake nema.

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, a yayin taron ne kwamitin wanda ya hada mabiya addinin Kirista da Musulmi ya tattauna matsalolin da ke hana ruwa gudu wajen samun zaman lafiya a kasar nan.

A jawabinsa, Sarkin Musulmi ya kalubalanci shugabannin da cewa su koma wa littatafan su masu tsarki don samun ginshikin shugabanci na gari.

A cewarsa, muddin aka rasa kyakkyawan shugabanci to za a rasa zaman lafiya da hakan zai tarwatsa duk wani hadin kai a tsakanin al’umma. A farko tun kafin taron ne Sarkin Musulmin ya jagoranci bude wata hanya a garin Gombe da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya gina kuma aka sanya mata sunansa a Unguwar Gandu da ke bayan gidan Sarkin Gombe.

Related posts

Leave a Comment