Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ha?in kan ?asar da tsaronta, “su ne abin da zan ci gaba da sakawa a gaba ko bayan na sauka daga mulki” a 2023.
Shugaban ya fa?i hakan ne yayin da yake tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyarsu ta APC ?ar?ashin jagorancin shugabanta na ?asa Sanata Abdullahi Adamu ranar Juma’a.
“Ina gode muku baki ?aya game da rawar da kuka taka, na farko kan shirin babban taronmu na ?asa a farkon wannan shekarar, da kuma za?en fitar da gwani daga baya,” in ji Buhari.
Kazalika, shugaban ya ce abin da suka fi sakawa a gaba shi ne ha?in kan APC kafin komai.
“A wajenmu ha?in kan jam’iyya ne farko, burikanmu kuma na biyu. Na ji da?i sosai da yadda kuka yi za?in da ya fi dacewa sama da son zuciyarku.”
Haka nan, Buhari ya ce har yanzu ba zai ce komai ba game da Sanata Kashim Shettima, mataimakin ?an takarar shugaban ?asa na APC, “har sai ranar da zan mi?a musu mulki”, yana mai cewa “na san ba zai ba mu kunya ba”.
