Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce noman taba na haddasa matsalar karancin abinci da kayan abinci mai gina jiki a akasarin yankunan Afirka.
Cikin wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai domin bikin ranar yaki da shan taba sigari ta duniya, daraktar WHO a Afirka, Dr Matshidiso Moeti ta ce ana amfani da gonakin da ya kamata a noma kayan amfanin gona wajen noma taba lamarin da ke lalata tsarin rayuwa tsakanin halittu.
Moeti ta kara da cewa “muna fuskantar ?alubale babba ta ?angaren abinci da abinci mai gina jiki sanadiyyar ?aruwar noman taba a yankin Afirka. A shekarun baya-bayan nan, noman taba ya koma Afirka saboda ?aruwar neman taba sigari a yankin.”
“Kusan mutum miliyan 828 ne ke fama da yunwa a fa?in duniya. Daga ciki, mutum miliyan 278 – kashi 20 cikin 100 suna Afirka. Kashi 57.9 cikin 100 na al’umma a Afirka suna fama da gagarumar matsalar ?arancin abinci.”
