Ganawar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da ?ungiyar ?wadago game da batun janye tallafin mai ta tashi baran-baran ba tare da cimma wata matsaya ba.
Nasir Kabiru, Sakataren tsare-tsare na NLC ne ya tabbatar wa BBC hakan inda ya ce ?ungiyarsu sam ba ta amince da tsare-tsaren da gwamnati ta yi ba game da janye tallafin na man fetur.
A cewarsa, bu?atarsu ita ce a inganta sufuri a kuma yalwata rayuwar ma’aikata kafin a soma aiwatar da tsarin.
An dai shiga tattaunawar ce da ?arfe 4 na yammacin yau Laraba a Fadar shugaban ?asa da ke Abuja, babban birnin ?asar.
Ganawar ta samu wakilai daga ?angaren gwamnati da suka ha?a da Dele Alake, kakakin shugaba Bola Tinubu da kuma shugaban kamfanin mai na ?asar NNPC, Mele Kyari.
Sauran jami’an gwamnatin sun ha?a da Gwamnan Babban banki, Godwin Emefiele da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole.
A nata ?angaren, ha?a??iyar ?ungiyar ?wadago ta samu wakilcin shugaban NLC, Joe Ajaero da shugaban TUC, Festus Osifo.
