Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero ya bayyana cewar a magana ta gaskiya idan za’a yi to gwamnatin jihar Kaduna ?ar?ashin jagorancin El Rufa’i ta fadi warwas ta fuskoki da dama.
Ramalan Yero ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan rediyon BBC Hausa ya yi dashi dangane da yadda siyasar Jihar Kaduna ke tafiya a yanzu.
Ya cigaba da cewar idan aka yi la’akari da irin cika baki da alkawarrun da APC suka yi a lokacin ya?in neman zabe musanman akan harkar tsaro to babu shakka gwamnati ta gaza kai banten ta.
Dangane da batun zargin da ake yi wa gwamnatin PDP lokacin mulkinshi na cewar ta yi aringizon daukar ma’aikata kuwa, Ramalan Yero yace ko ka?an wannan magana ba haka take ba, gwamnati ba kamar kamfani ba ce ballantana ta yi aringizon Ma’aikata.
Ramalan Yero ya kuma bayyana cewar Gwamnatin shi a baya ta yi rawar gani ta fuskar aikace-aikace, domin ayyukanta ya shafi dukkanin kananan hukumomi 23 ne Jihar sa?anin APC da a yanzu take aiki a garin Kaduna da Zariya kawai.
