Ni Ne Halastaccen Shugaban Najeriya – Peter Obi

?an takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party a babban zaben 2023, Peter Obi, ya ayyana cewa dole ne ya zama shugaban kasa a Najeriya. Mista Obi, wanda ya zo na uku a za?en shugaban kasa, ya yi wannan furucin ne a wurin kaddamar da littafinsa mai suna, “Peter Obi: Many voices, one Perspectives”, a Awka, babban birnin jihar Anambra ranar Jumu’a.

An shirya taron kaddamar da littafin ne da nufin tara ku?in ?aukar nauyin ?arar da ya shigar gaban Kotun za?e, yana kalubalantar nasarar Bola Tinubu.

“Duk wanda ke tunanin zan sa kafa na bar ?asar nan yana ?ata lokacinsa ne, ya zama dole na zama shugaban ?asa a Najeriya, idan ba yau ba, nan gaba.” “Sauran masu son zama (shugaban kasa) su fito su gaya mana gaskiyar abinda suke fatan yi da kuma hanyar da zasu bi su aiwatar.

Nan ?asata ce, banda shaidar zama a wata ?asa.” “Saboda haka dole na zama shugaban kasa, idan ba yanzu ba, nan gaba, ban ?osa ba kuma ba sauri nake ba, na sadaukar da kaina domin ganin Najeriya ta gyaru.”

Haka nan, tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce zasu girmama duk hukuncin da Kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke a ?arar da ake ci gaba da muhawara kanta.

“Muna son zaman lafiya, ba wani ?an siyasa da zamu yi jayayya da shi, kar guiwarku ta yi sanyi game da hakurin da nake baiwa wasu mutane. A matsayin matasa ba zamu yi fa?a da iyayenmu ba ko da kuwa muna kan gaskiya.”

Related posts

Leave a Comment