Kaduna: Uba Sani Ya Bayyana Aniyarsa Ta Zama Gwamna

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa Sanata Uba Sani ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023 dake tafe.

Sanata Uba Sani ya bayyana ra’ayin sa na zama gwamnan Kaduna ne a hedikwatar jam’iyyar APC dake Kaduna ranar Talata.

Wannan taro ya samu halarcin jigajigan ?an siyasa da ke jihar musamman ?a?an jam’iyyar APC

A jawabin da yayi a wajen bayyana burin sa, sanata Uba Sani ya ce, shine ya fi dacewa ya gaji gwamna Nasir El-Rufai ganin irin kusancin dake tsakanin sa da shi.

” Tun da aka kafa gwamnati a Kaduna a 2015 muke tare kud da kud da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai. Muna tare muna ganin ayyukan cigaba da ya kawo jihar wanda ba a taba yin irin sa ba. Hakan ya bani daman sanin abinda jihar ke ciki da yadda za dora daga inda aka tsaya idan Allah ya bamu sa’ a. Sannan zamu cigaba da kyawawan ayyukan da gwamna El-Rufai ya yi don ci gaban jihar mu

Bayan haka sanata Uba ya godewa mutanen jihar Kaduna da ?a?an jam’iyyar kan nuna masa soyayya da suka yi a lokaci da ya bayyana ra’ayin sa.

A karshe ya yi fatan Allah ya su sa a ya kuma sa yi wa mutanen jihar Kaduna Albarka da fatan samun zaman lafiya.

Related posts

Leave a Comment