Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe akalla mutane bakwai a kauyen Warkan na yankin Atyap a karamar hukumar Zangon Kataf da ke kudancin jihar Kaduna.
An tattaro cewa ‘yan bindigan sun kuma kona gidaje da dama da salwantar da dukiyoyi masu yawa, yayin da wadanda suka samu raunuka ba za su misaltu ba.
Majiyarmu ta ce maharan sun durfafi kauyen a lokacin da suka kai harin suka ci karen su ba babbaka, yayin da mahukunta ke kokarin gano yawan mutanen da suka samu raunuka.
Rahoton ya ce abin bakin ciki shine yadda mahukunta ba sa daukan matakai masu tsauri da zasu dakile irin wadannan hare-haren da suke faruwa na tsawon lokaci musamman a yankin Atyap.
“Mun gagara fahimtar yadda ake kai hare-hare akai-akai musamman a wannan yanki namu na Atyap, abin takaici shine yadda gwamnati a matakin jiha da ta tarayya suka gagara daukan tsauraran matakai don dakile wadannan hare-hare.” In ji majiyar.
Kokarin da aka yi don samun martani dangane da harin daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Muhammad Jalige ya ci tura. Yayin da kwamishinan Tsaron Cikin Gida Samuel Aruwan shi ma ba a same shi ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoton.
