Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu mazauna babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja sun bukaci wata babbar kotu a birnin ta dakatar da rantsar da zababben shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu.
Mutanen da suka samu wakilcin lauyoyi kamar su, Anyaegbunam Ubaka Okoye, David Aondover Adzer, Jeffrey Oheobeh Ucheh, Osang Paul da Chibuke Nwachukwu, suna neman kotun ta dakatar da alkalin alkalan kasar, ko ma wani, daga rantsar da duk wani wanda ya yi takara a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin shugaban kasa ko mataimaki.
Sun ce bukatar hakan ta zama wajibi har sai an warware korafe-korafen zabe da ke gaban kotu, daidai da tanadin sashi na 134, karanmin sashi na 2.
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na Labour wadanda suka zo na 2 da na 3 suna kalubalantar sakamakon.
Kotu ta fara sauraron kararrakin da ke kalubalantar nasarar Tinubu a ‘yan kwanakin da suka gabata.
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar da cewa Shugaban Nijeriya. mai barin gado Muhammadu Buhari da mai dakin sa sun bar fadar gidan shugaban kasa ta Villa zuwa wani ?angaren gidan da ake kira Glass House.
Kamar yadda doka ta tsara duk sanda za a mika mulki ga wata sabuwar gwamnati, shugaba mai barin gado zai bar Villa zuwa wannan bangaren na Glass House domin mika mulki ga sabuwar gwamnati.
Dokar mulkin Nijeriya ta tsara cewa ko wane shugaban kasa ba zai haure shekaru hudu akan karagar mulkin Nijeriya ba, Wanda hakan ke nufin duk bayan shekaru hudu za’a gudanar da zaben Shugaban kasa da na yan majalisun Dattawa da na majalisun wakilai duk bayan shekaru hudu.
Dokar ta bada dama ga duk Shugaban da ya yi shekaru hudu akan karagar mulkin Nijeriya ya nada ikon ya sake neman karin wasu shekaru hudun a karo na biyu amma fa daga su ba kari.
Yanzu haka dai Shugaba Buhari ya cinye shekaru takwas akan kujerar mulkin Nijeriya wanda hakan yasa dole ya sauka a ranar 29 ga watan mayu 2023 ya mikawa sabuwar gwamnati kamar yadda dokar kasa ta tsara.
