NBC Ta Haramta Sa Wakar Ado Gwanja A Gidajen Talabijin Da Rediyo


Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta ?asa, NBC ta hana sanya sabuwar wa?ar Ado Gwanja mai taken ‘warr’ a gidajen Radiyo da Talabijin na ?asar .

Hakan ya zo ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai ?auke da kwanan watan 6 ga watan Satumba, 2022.

Sanarwar da tace an dakatar da sanya wakar ne a radiyo da talabijin sabo da wasu kalamai da ya ke yi a cikin baitocin wa?ar, wa?anda su ka sa?a da dokokin hukumar da kuma al’adar Hausawa.

Sanarwar tace wa?annan baitoci da suke cikin wakar ta Warr sun sa?awa sashe na 3, 18, 2(c) na hukumar dake kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC.

Sa?awa wannan umarni na hukumar NBC ga kafafen ya?a labarai na rediyo da talabijin zai iya sanyawa a hukunta kafar ya?a labaran, inji sanarwar.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa sabbin wakoki biyu da Gwanja ya fitar da su ‘warr’ da ‘chas’ na nan na shan suka duba da yadda yanayin wa?o?in ke zama barazana ga tarbiyya.

Jaridar nan ta gano cewa Gwanja har zagi ya ke yi a cikin wasu baitukan wakar ‘warr’ ?in, inda hakan ya sa?awa addini da al’adar mutanen Kano.

Hakan ce ma ta sanya wasu lauyoyi guda 9, su ka shigar da ?orafi gaban Kotun Shari’ar Muslunci, wacce tuni ta baiwa ?an sanda damar bincikar Gwanja ?in da sauran mutane 6 bayan ?orafin da lauyoyin su ka shigar.

Related posts

Leave a Comment