APC Na Duba Yiwuwar Dage Babban Taron Gangamin Jam’iyya

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar da alamun taron gangamin jam’iyyar APC da aka shirya yi ranar 26 ga Febrairu, 2022, ba zai yiwu ba saboda wasu dalilai.

A cewar rahoton ThisDay, ana shirin dage taron gangamin da makwanni biyu duk da cewa jam’iyyar bata bayyana hakan ba, wata majiya tace shugabannin jam’iyyar da Gwamnoni zasu tattauna da Shugaba Muhammadu Buhari don bada shawaran dage taron.

Ana kyautata zaton cewa rana 12 ga Maris za’a mayar. Majiyar tace: “An dage taron gangamin da makwanni biyu amma ba’a sanar ba tukun.

Kwamitin rikon kwarya da gwamnoni zasu gana da Shugaban kasa don bashi shawarar sabuwar rana.”

Hakazalika wani tsohon dan kwamitin gudanarwan jam’iyyar, wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace ko shakka babu ba za’ayi taron ba. Yace: “Akwai abubuwan da ya kamata ayi kafin taron gangami ya yiwu ranar 26 ga Febrairu kuma ba’ayi hakan ba.

Related posts

Leave a Comment