Al’ummar mazabar Kawo dake yankin ?aramar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna sun fito kwai da ?war?wata inda suka nuna goyon baya ga ?an takarar kujerar majalisar dokokin jihar Aliyu Haruna Chakis na jam’iyya mai kayan marmari ta NNPP.
Daraktan ya?a labarai na Ali Chakis Abdullahi AG ya bayyana hakan a wata takardar sanarwa da ya fitar wadda aka rarraba wa manema labarai a Kaduna.
Abdullahi AG ya cigaba da cewa ko shakka babu Honorabul Aliyu Haruna Chakis ya yi rawar gani a zaman majalisar dokokin jihar Kaduna da ya yi, da kuma mu?amin mai ba Gwamna shawara kan harkokin Matasa.
“Babu shakka mutane irin su Ali Chakis ake da bu?ata a majalisa domin sun yi an gani, kuma lalle jama’a za su samu kyakkyawan wakilci idan aka za?e shi ?an majalisa a 2023”
