Ku Kakkabe Ragowar Boko Haram Dake Sambisa – Umarnin Shugaban Soji Ga Sojoji

Shugaban Sojojin Najeriya, Janar Farouk Yahaya ya nemi dakarun sojojin su shiga su kakkabe sauran Burbushin Boko Haram da ya rage.

Ya basu tabbacin samar da kayan aiki da jin dadinsu.

Ya bayyana hakane ranar Asabar a ziyarar da ya kaiwa Bataliya ta Sojoji dake Damaturu a jihar Yobe.

Ya baiwa sojojin tabbacin cewa, duk wanda yayi bajinta zai samu girmamawa ta musamman.

Related posts

Leave a Comment