Yankin Arewa Ba Ya Tsoron Rabewar Najeriya – Matasan Arewa

An bayyana cewar ko ka?an yankin Arewacin Najeriya ba ya tsoro ko fargabar rabewar Najeriya kamar yadda sashin Kudanci ke ta han?oro akai, sai dai kawai yankin yana cizawa gami da hurawa ne domin samun maslaha.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin ?aya daga cikin shugabannin kungiyar Matasan Arewa Alhaji Kamal Nasiha Funtuwa a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a garin Kaduna.

Kamal Funtuwa ya kara da cewar hangen nesa na jama’ar Arewa ba kamar na jama’ar kudancin Najeriya ne, domin tsari da tarbiyar arewa ya sanya yankin ya fahimci cewar zaman tare ya fi akan zaman ‘yan marina, domin tabbas kowane yanki a kasar yana bukatar ?an uwanshi, amma wannan ba yana nufin Arewa na tsoron wargajewar Najeriya bane idan bu?atar hakan ta taso inji shi.

Shugaban Matasan ya bayyana cewar al’ada ce ta mutanen Kudancin Najeriya duk lokacin da ya zamana ?an Arewa ne ke mulki zasu yi tada hankali da kiran a raba ?asa, amma da zarar mulki ya koma hannun ‘yan kudu shikenan magana ta kare ba zaka sake jin su ba, inda ya bada misali da abubuwan da suka faru a lokacin mulkin Abacha na kiran a raba ?asa da aka rin?a yi, amma lokacin da mulkin ya koma hannun Obasanjo shikenan kowa ya yi shiru, a lokacin da mulkin ya dawo Arewa hannun ‘Yaraduwa suka cigaba da kiran raba ?asa, lokacin da mulkin ya dawo hannun Jonathan sai kowa ya yi shiru.

Kamal Nasiha Funtuwa ya ce makomar Najeriya a yanzu na hannun ‘yan Najeriya ne, idan ‘Yan Najeriya sun amince da yin haka babu wata matsala, musanman a gyaran fuska da ake yi na kundin tsarin mulki, idan ta kama ayi kuriar jin ra’ayin jama’a ne akan haka babu matsala Arewa a shirye take.

Related posts

Leave a Comment