Na Kusan Haukacewa Bayan Kisan Da IPOB Suka Yi Wa Matata Da ‘Ya’yana -Jibril

Mutumin da IPOB suka kashe wa matarsa mai ciki wata tara da kuma ?a?ansa hu?u a jihar Anambra ya ce ya ji kamar ya haukace saboda tashin hankalin da ya shiga.

Wasu ?an bindiga da ake zargin ?an ?ungiyar IPOB ne suka kai hari suka kashe mutum 12, ciki har da mace mai ciki wata tara, Harira Jibril da ?a?anta hu?u.

Mijin matar kuma mahaifin ?a?an dukkanin mata da aka kashe a harin ya shaida wa BBC cewa an kashe matarsa ne da ?a?ansa a lokacin da suke kan hanyar dawowa daga ziyarar da ta kai, tare da ?a?anta a yankin Orumba ta arewa a jihar Anambra.

“Na shiga tashin hankali, saura ka?an na haukace – kamar an saka ni cikin wuta, haka nake ji saboda zafin da nake ji,” in ji Jibril Ahmed mijin matar.

“Yanzu ina zan fara – yaya zan yi aure har na samu ?a?an da Allah ya ba ni wa?anda har sun yi nisa da karatu.”

“Yarana suna da basira amma ga shi yanzu irin ?arnar da aka yi min, kawai na yi tawakalli ga Allah – Allah zai saka min,” in ji shi.

“An caje ni naira dubu 170 na daukar gawarsu zuwa jihar Adamawa sannan na biya naira dubu 30 a dakin ajiye gawa,” in ji Jibril Ahmed.

Ya ce a cikin satin nan matarsa za ta haihu amma aka kashe ta.

“Iyayen matata sun shiga tashin hankali kuma ina ?o?arin tafiya da gawarta domin a binne ta garin iyayenta.”

?an sandan Najeriya sun ce sun kama ?an bindigar da suka aikata kisan na mutum 12 da suka ?unshi har da mace mai ciki da ?a?anta hu?u.

Related posts

Leave a Comment