Majalisa Ta Amince Buhari Ya Karbo Bashin Tiriliyan Biyu Da Rabi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar Dattawa a ranar Laraba, ta amince da bu?atar shugaban ?asa Muhammadu Buhari, na kar?o bashin tiriliyan N2.3tr domin cike gi?in kasafin ku?in 2021 kamar yadda ya bukata.

Amincewar ta biyo bayan nazari da sanatocin suka yi akan rahoton kwamitin dake kula da bashin da ake bin Najeriya a gida da waje, wanda Sanata Clifford Ordia (PDP, Edo), yake jagoranta.

Sanatocin sun amince da bu?atar shugaba Buhari na fitar da yuro biliyan $3b amma kada ya wuce $6.1 billion a kasuwar duniya domin aiwatar da gi?in kasafin ku?i na 2.3 tiriliyan.

Hakanan kuma sanatocin sun umarci ?usoshin Gwamnatin tarayya da abun ya shafa su kaiwa majalisa takardar dake ?unshe da yawan ku?in Amurka da aka samar da wa?anda suka kar?a bisa amincewa da amso wannan bashin da kuma yadda ake hada-hadar ku?in a kasuwa.

A watan Mayun da ya gabata ne, shugaba Buhari ya nemi amincewar yan majalisa wajen samar da wasu ku?a?e daga ?angarori da dama.

Related posts

Leave a Comment