Kaduna: Dalilina Na Neman Deligates Su Dawo Mini Da Kudina – ABG

?an takarar kujerar Majalisar dokokin tarayya mai wakiltar mazabar ?aramar hukumar Kaduna ta Arewa a karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Shehu ABG ya koka da yadda masu za?en ‘yan takara wato Deligates a Jam’iyyar suka yi sa?a da mugun zare a yayin za?en fidda gwani da ya gudana.

?an siyasar ya bayyana hakan ne a yayin tattunawar su da wakilinmu a garin Kaduna.

ABG ya ce ya ya bayar da tukwicin ma?udan ku?a?e ga Deligates da ya kai kimanin Naira Miliyan 3 da rabi ga kowane Deligates domin samun nasarar zabe, amma a karshe bayan kar?ar kudaden sai suka juya mishi baya.

Shehu ABG ya ?ara da cewar ganin irin wannan cin amana da suka yi mishi ne ya sanya ya bukaci da su dawo mishi da ku?a?en da ya basu, domin babu ?ira ba abin da zai ci gawayi, kuma tuni suka dawo mishi da ku?a?en da ya bayar.

“Ina amfani da wannan dama wajen yin kira ga dukkanin ‘yan takara duk wanda ya san ya bada ku?in shi domin a za?e shi kuma aka sa?a yarjejeniyar da aka yi to lallai ya nemi a dawo mishi da ku?in sa.

Related posts

Leave a Comment