Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano a ranar Talata ta yi watsi da umarnin da ta bayar a baya na hana shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Shehu Sagagi da ya ri?a nuna kan sa a matsayin shugaban jam’iyar a jihar.
Ana zargin dai Sagagi yana biyayya ga tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso.
A ranar 17 ga Mayu ne dai, Justice A.M. Liman ya bayar da umarnin dokar wucin gadi ta hana shugabannin PDP da Sagagi ke jagoranta a Kano yin duk wani iko har sai an saurari koke-koken kudirin nasa.
Wani Bello Bichi ne ya kai karar INEC da PDP da wasu mutum 40 gaban kotun.
Da yake ba da umarnin a ranar Talata, Mai shari’a Liman ya ce wanda ya shigar da kara, Bello Bichi, ya yaudari kotun da cewa akwai gaggawa a kan lamarin.
Ya ci gaba da cewa Bichi ba shi da hurumin shigar da ?arar saboda bai nuna hujjar cewa shi mamba ne a kwamitin zartarwa na jam’iyyar ba.
Don haka mai shari’a Liman ya ?age sauraren ?arar zuwa ranar 26 ga watan Mayu domin sauraren ?arar.
