Muna Jin Radadin Rashin Shugabanci Nagari A Kasa – Gwamnonin PDP

Gwamnonin PDP sunce suna Jin Radadin rashin shugabancin na gari da Gwamnatin APC take jagoranta a matsayin gwamnatin tarayya a sama, Shugaban Kungiyar gwamnonin Waziri Ibrahim Tambuwal Gwamnan Sokoto ya fadi haka kafin su fara taron su na gwamnonin a Jihar Bauchi.

Waziri Tambuwal yace Jamiiyyar PDP itace zata cire Yan Najeriya daga cikin kangin da suka shiga a dalilin rashin iya shugabanci tare da rashin kwarewa a fagen siyasar da zata ciyar da yan’Najeriya gaba da kuma cire su a kuncin rayuwa cikin kankanin lokaci

Shugaban gwamnonin Jamiiyyar PDP yace sunzo Bauchi a ci gaba da taronsu na gano bakin zaren da Yan’Jam’iyyar APC suka jefa al’ummar kasa baki daya, rashin tsaro ya karo ga tsadar rayuwa, ga tattalin arzikin kasan ya tabarbare halin yanzu, a cewar shi jamiyyarau zata Kai Najeriya tudun mun tsira, a zaben gamagari nan gaba.

Shugaban ya yabawa Gwamnan Bauchi Wanda shine Mai masaukin baki kannirin ayyukan da take gudanarwa a dukkan fadin jihar, cewa dole ne a jinjina mashi da na mijin kokari a cikin lokaci kadan, yace mutanen Bauchi sunyi sa’ar Gwamnan haziki jajirtacce.

Yace duk masu guduwa daga jamiyyar PDP suna yin hakan ne don su sami mafaka akan irin al’mundahana tare da ta’asar da suka tafka, domin kar a bankado laifinsu da kuma fuskantar bincike na tsawon lokacin da sukayi suna mulki a jihohinsu.

Hakanan, yace su suna nan daram a cikin jamiyyar su babu gudu babu ja da baya, kuma ya fadi cewa Yan Najeriya sunyi amanna da PDP lokaci kawai suke jira aga yadda zasu kwace mulkin Najeriya a zaben dubu biyu da ashirin da uku 2023

Daga karshe yace ana sa ran zasu tattauna batutuwan da suka shafi kasa da al’ummar Najeriya kai tsaye, a zaman taron na Bauchi, musamman kan gyaran kundin tsarin mulki na kasa da kuma kundin tsarin zabe da ake ta kokarin yi mashi garan bawul, don amfanin al’ummar Najeriya baki daya.
Kana Shugaban ya kaddamar da Sabon ginin gidan gwamnatin Jihar Bauchin da Gwamna Bala ya karisa ginawa a kwana nan

Related posts

Leave a Comment