Wasu hare-hare ta sama da dakarun sojin Najeriya suka kai ranar 20 ga watan Disamba a ?auyen Mantari an yankin Gezuwa da ke cikin ?aramar hukumar Bama a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya yi sanadin kashe wasu manyan kwamandojin ?ungiyar Boko Haram.
A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin sama na ?asar Air Commodore Edward Gabkwet ya sanya wa hannu ya ce harin ya yi sanadin mutuwar manyan kwamandojin ?ungiyar da suka ha?ar da Khaids Abbah Tukur da Maimusari da kuma Bakura Jega, tare da wasu ‘yan ?ungiyar da dama.
Labarin ya fito ne jim ka?an bayan da manyan hafsoshin sojin ?asa da na sama suka hallara a birnin Maiduguri ranar Lahadi da safe, domin yin shagulgulan bukukuwan Kirsimeti tare da sauran dakarun da ke fagen daga.
Sanarwar ta ci gaba da cewa dakarun sojin saman sun ?addamar da harin ne bayan da suka samu bayanan sirri da ke cewa wani kwamandan mayakan Boko Haram mai suna Ikirima, ya shirya dakarunsa ri?e da bindigogi a ?auyen Mantari, tare da wasu ‘yan tayar da ?ayar bayan sun taru a waje guda a kan babura da kekuna.
”Nan take kuma aka bayar da umarnin ?addamar da hari kansu, lamarin da ya haddasa kashe manyan kwamandojin tare da wasu maya?an ?ungiyar akalla 100”, kamar yadda sanarawar ta bayyana.
Bayan harin ne kuma wasu daga cikin maya?an suka koma wajen da lamarin ya faru domin ?aukar gawarwakin ‘yan uwansu, hakan ne kuma ya bai wa dakarun sojin damar sake far musu tare da kashe wasu da dama cikinsu.
Manyan hafsoshin sojin sama da na ?asa na ?asar sun yaba da wannan ?o?ori na dakarun tare da sauran jami’an tsaro ?ar?ashin Operation Ha?in Kai, da kuma ci gaban da suke samu a ya?in da suke yi da ?ungiyar Boko Haram.
BBC Hausa
