Matsalar Najeriya: Gwamnonin PDP Na Taro A Bauchi

Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamnonin babbar jam’iyyar adawa ta PDP suna gudanar da wani gagarumin taro domin lalubo hanyar magance matsalar tsaro dake addabar Najeriya.

Gwamnonin 13 suna taron ne don tattaunawa kan halin da kasar ke ciki a yanzu haka da kuma na jihohinsu.

Batutuwan da suka shafi rashin aikin yi da yanayin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki da halin da dimokradiyya ke ciki kamar batun sauya dokokin zabe da na kundin tsarin mulki ne manya da za su mamaye taron na yay.

Sannan a yayin taron gwamnonin za su tuhumi gwamnatun tarayya kan yadda take tunkarar matsalar tsaro.

Kazalika za su bijiro da matakan da suke ganin za a bi a warware matsalolin.

Gwamnonin na PDP za kuma su karbi rahotanni daga wasu kwamitocin da ke aiki kan yadda za a yi wa jam’iyyar garambawul

Daga cikin abubuwan da gwamnonin na PDP za su yi har da kaddamar da sabon ofishin gwamna.

Manyan Sarakunan gargajiya na Jihar da suka hada da na Bauchi da Ningi da Katagum da Dass duka sun halarci taron

Related posts

Leave a Comment