Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-?aci kan batun samar da abinci a ?asar.
Mai magana da yawun shugaban ?asar Dele Alake, ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gwamnatin ?asar da ke Abuja.
Shugaban ?asar ya bayar da umarnin mayar da duka al’amuran da suka shafi samar da abinci da ruwan sha, a matsayin manyan abubuwan dogaron rayuwa zuwa ?ar?ashin kulawar majalisar tsaro ta ?asa.
Alake ya ce umarnin na cikin tsare-tsaren gwamnatin Tinubu na tabbatar da tallafa wa masu ?aramin ?arfi a ?asar.
Ya ce Shugaban ya damu kan yadda farashin kayan abinci ke ?aruwa da yadda hakan ke shafar talakawan ?asar.
Shugaban ya kuma bayar da umarnin gaggauta bai wa manoman ?asar taki da irin shuka domin rage musu ra?adin cire tallafin man fetur.
Ya ?ara da cewa “Dole hukumomin ayyukan gona da ta ruwan sha su yi aiki tare domin tabbatar da ingantuwar noman rani a ?asar don tabbatar da samar wadataccen abinci a ?asar a kowanne yanayin shekara”.
