Saudiyya: Sheikh Shuraim Ya Ajiye Limancin Ka’abah

Rahotannin dake shigo mana daga ?asar Saudiyya na bayyana cewar Limamin din-din-din na masallacin Makka Sheikh Saud Ash Shuraim ya ajiye aikin limancin masallaci.

Cikin wata sanarwa da shaifin Haramain Sharifainya fitar a shafunsa na sada zumunta, ya ce Shuraim ya yi murabus ?in ne bayan shafe shekaru 32 yana gudanar da aikin limanci.

Imam Shuraim ya ce wasu dalilansu na kai da kai ne suka sanya shi ajiye ma?amin shugabancin limanci.

Zai iya komawa ya ci gaba da jagoranin sallar tarawihi a matsayin ba?on limami, wanda za a sanar da dalilan haka nan da makonni masu zuwa.

Related posts

Leave a Comment