Rahoton dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Kotun daukaka kara da ke zama a Kano ta soke hukuncin babban kotu da ta bayyana Muhammad Abacha matsayin ‘dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP.
Kotun daukaka karar ta yi umarnin cewa, Sadiq Wali, wanda a baya hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta ayyana shi matsayin ‘dan takara, shi ne sahihin ‘dan takarar.
A hukuncin da alkalai uku suka yanke, Mai Shari’a Usman Musale, kotun ta yanke hukuncin cewa a bayyane yake NEC din jam’iyyar za ta iya zaben fidda gwanin jam’iyyar kuma tunda Abacha bai yi zaben da NEC ta samar da Wali ba, bashi da hurumin kalubalantar zaben.
