Rahotannin dake shigo mana daga kasar Rasha na bayyana cewar kasar ta ce ta kashe adadi mai yawa na abin da ta kira ‘sojan haya na kasashen waje tare da lalata makaman da aka shigo da su daga kasashen waje a harin da ta kai wa wani sansanin soji da ke Yavoric a yammacin Ukraine.
Jami’an Ukraine din sun cemutane akalla35 ne suka mutu.
Da sanyin safiyar Lahadi ne aka harba makamai mazu linzami asansanin da ke kusa da kan iyaka da kasar Poland.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce za a ci gaba da kai hare-haren.
Magajin garin Lviv ya ce ya?in ya kusan shafar ?asashe mambobin Nato, yana mai ?ara kiran sanya dokar hana shawagin jirage a Ukraine.
