Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Bude Wa Motar Fasinja Wuta

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar cewa an kashe fasinjoji biyar sannan wasu uku sun ji munanan rauni bayan yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota a hanyar Yan Tumaki zuwa Danmusa da ke jihar a safiyar Asabar.

Karamar hukumar Danmusa na daya daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro a Katsina, inda ta raba iyaka da dajin Rugu da yankuna irin su Safana, Kankara da garuruwan jihar Zamfara inda ‘yan Bindiga ke yin barna sosai.

Wani shaidar gani da ido wanda ya bayyana sunansa a matsayin Musa, ya shaida cewa yawancin fasinjojin sun fito ne daga Benin a jihar Edo yayin da daya yake dawowa daga birnin tarayya Abuja inda ya je kai odar kaji. Ya ce fasinjojin yan asalin Gobirawa da Kaigar Malamai da ke jihar Katsina ne.

“Motar, kirar Golf ce ta bar Yantumaki zuwa garin Danmusa da safiyar. Fasinjojin sun kwana a Yantumaki saboda isowar dare suka yi. Da safe, sai suka dauki mota zuwa garin Danmusa inda daga nan za su hau babura zuwa kauyukansu. “Amma sai aka farma motar yan mintuna kadan bayan sun bar Yantumaki.

Abun da ya faru shine cewa yan bindiga sun hango motar sannan suka yi kokarin tsayar da ita amma direban ya ki tsayawa, hakan ya sa yan bindagar suka bude masu wuta. Motar ta yi yar dungure sannan ta daki wata bishiya.”

Musa ya ce yan bindigar sun tsere a lokacin da hatsarin ya afku. ya kara da cewa: “Wasu bayin Allah ne suka sanar da yan sanda a Danmusa sannan suka kwashi gawarwakin da kuma kai mutane uku da suka jikkata asibiti.

Tuni muka birne mamatan yayin da sauran uku ke samun kulawa a asibiti.”

Wata majiya da ke zama a yankin wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce yan bindigar na kai hare-hare ne domin yin ramuwar gayya kan barin wuta da jami’an tsaro ke yi masu. “Hatta da kisan fasinjojin an ce ‘yan bindigar sun fusata ne saboda ‘yan sanda da sojoji sun hana su satar shanu da yawa a ranar Alhamis din da ta gabata.”

Ya ce: “’Yan bindigar sun yi nasarar satar shanun amma rundunar hadin guiwa ta jami’an tsaro ta kama shanun daga hannun su. Haka kuma an kashe wasu daga cikin ‘yan Bindigar a cikin lamarin.”

Ya bayyana cewa kwanan nan yan sanda suka kona sansanin yan bindiga a yankin wanda mai yiwuwa shine ya fusata yan bindigar. Mallam Musa ya kuma tabbatar da labarin kwato shanun kuma ya ce hakan na iya zama dalilin kai harin na rashin tausayi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Gambo Isa, ya tabbatar da faruwar al’amarin a ranar Lahadi. Ya ce: “Eh, gaskiya ne. Lamarin ya faru ne jiya da safe. ‘Yan bindigar sun budewa motar wuta ne domin nuna adawa da kashe daya daga cikinsu da tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin kwamandan Danmusa suka yi musu bayan da suka dakile harin tare da kwato shanu sama da 30 da aka sace.

Related posts

Leave a Comment