Gwamnatin kasar Ukraine ta garga?i da kakkausan harshe ga ?asar Iran da cewa ‘asarar’ da za ta tafka sakamakon goya wa Rasha baya a ya?in da take a Ukraine ya fi ‘ribar’ da za ta samu na yin hakan.
Garga?in na zuwa ne bayan da a karon farko Iran ta amince cewa ta sayar wa da Rasha jirage marasa matu?a, to sai dai tana mai cewa ta yi hakan ne tun kafin fara ya?in Ukraine.
?asashen yamma na zargin Rasha da amfani da jirage marasa matu?a na Iran wajen kai hare-hare kan gine-gine masu mihimmanci a Ukraine, tare zargin cewa sojojin Iran na horas da dakarun Rasha kan yadda za su yi amfani da jiragen, zarge-zargen da Rasha da kuma Iran ?in suka sha musantawa.
To sai dai a ranar Asabar ministan harkokin wajen ?asar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya shaida wa manema labarai a Tehran cewa ?asarsa ta tura wasu jiragen marasa matuka da ba su da yawa zuwa Rasha, yana mai cewa sun yi hakan ne watanni kafin fara ya?in Ukraine.
