Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce har yanzu shi ?an jam’iyyar PDP ne duk da cewa ya soma tattaunawa da jam’iyyar NNPP domin sauya sheka zuwa can.
A hirarsa da BBC, jagoran kungiyar siyasa ta Kwankwasiyya ya ce a makwannin da suka gabata ne suka kaddamar da wata sabuwar kungiya mai suna ‘The National Movement’, bayan nan ne aka samar da jam’iyyar NNPP.
Ya ce akwai bukatar nazari kan abin da kasa za ta sauya sannan ta samu sabon alkibla, sai dai yana mai jaddada cewa har yanzu ya na nan a cikin jam’iyyar PDP bai fita daga cikinta ba.
“Har yanzu da na ke magana da kai muna tsakanin kungiya da jam’iyya sannan ban fita daga cikin jam’iyyar PDP ba, kuma wannan kungiya ta hade ne da jam’iyyar NNPP.
Duk ranar da zan bar PDP ku ne na farko da za ku sani saboda abubuwan ne a tsare su ke mu na komai cikin tsanaki.”
